in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wane mataki Rasha za ta dauka don mayar da martani ga sabon takunkumin da Amurka ta kakaba mata
2018-08-23 14:19:33 cri
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana a jiya Laraba 22 ga wata cewa, sabon takunkumin da Amurka ta kakabawa Rasha ba shi da wani amfani ko kadan. Kuma ya yi kira ga gwamnatin Amurka, da ta fahimci cewa ba ta da wata nasara kan wannan manufa, yana mai kira ga Amurkan, da ta komawa hanyar da ta dace, ta gudanar da hadin kai tsakaninsu.

A ran 21 ga wata ne Amurka ta fara aiwatar da manufar kakabawa Rasha takunkumi a sabon zagaye, kan wasu jiragen ruwa ko kungiyoyi ko daidaikon mutane 'yan kasar ta Rasha, wadanda kuma za a daskaras da dukiyoyinsu dake Amurka, da hana Amurkawa yin ciniki da su.

Amurka ta ce dalilin sanya wadannan takunkumi shi ne gudanar da laifi kan Intanet, da ba da taimako ga kungiyoyin da Amurka ta riga ta sanyawa takunkumi, da tuhumar su kan mika man da aka tace a cikin wadannan jiragen ruwa, zuwa wasu jiragen ruwa masu dauke da tutar Korea ta arewa da sauransu.

An ce, tun daga farkon wannan wata, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta nuna cewa, Amurka ta tabbata cewa, Rasha ta sabawa dokar kasa da kasa, game da lamarin tsohon dan leken asiri na Rasha, wanda aka sanyawa guba a Birtaniya, matakin da ya sa ta sakawa Rasha wasu takunkumi, ciki hadda hana fitar da kayayyaki, da harkokin kimiyya dake shafar tsaron kasar zuwa Rasha.

An yi kiyasin cewa, ko da yake wannan takunkumin da Amurka ta kakabawa Rasha a ran 21 ga wata ba shi da karfi sosai, amma ya kasance matakin farko, a jerin takunkumin da Amurka za ta kakabawa Rasha.

Hakazalika, a ganin wasu masanan tattalin arziki, jerin takunkumin da Amurka da Turai suke kakabawa Rasha na tsawon lokaci, ya zama babban kalubale da tattalin arzikin Rasha ke fuskanta.

Ko da yake, Rasha ba ta da isasshen karfi na tinkarar irin wadannan kalubaloli, amma don cika alkawarin da ya yi yayin da yake ci gaba da wa'adinsa na shugaban kasar, jawabin shugaba Putin, da kuma matakan da ya dauka a kwanakin baya-baya, na bayyana niyyarsa ta mayar da martani mai karfi ga Amurka. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China