in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Sama da bakin haure 13,000 aka mayar da su kasashensu na asali daga Libya a 2018
2018-10-22 09:41:09 cri
Ofishin bada tallafi na MDD dake Libya ya sanar da cewa sama da bakin haure 13,000 hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa (IOM) ta kwashe tare da mayar da su kasashen na asali daga Libya a shekarar 2018.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Tweeter, hukumar ta ce, kimanin bakin haure 13,393 IOM ta mayar zuwa kasashensu na asali daga Libya karkashin shirin kwashe bakin haure don mayar da su kasashe 32.

Aikin kwashe bakin hauren wani bangare ne na shirin sa kai na hukumar ta IOM, da nufin tsara yadda za'a mayar da bakin hauren zuwa kasashensu na asali wadanda ke gararamba a kasar Libya.

Akwai matukar cunkoson bakin haure a wajen da aka kebe musu a Libya inda aka tsugunar da dubban bakin hauren wadanda jami'an tsaron tekun Libya suka ceto daga tekun kasar.

Libya ta kasance tamkar matattarar bakin haure ta barauniyar hanya wadanda ke neman tsallakawa kasashen Turai ta tekun Meditereniya sakamakon rashin tsaro da kuma tashin hankalin da ya daidaita kasar ta arewacin Afrika tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban Libyan marigayi Muammar Gaddafi a shekarar 2011. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China