in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morrocco ta bankado yunkuri 54,000 na bakin haure dake son shiga kasar cikin watanni 8 na farkon bana
2018-09-21 10:24:38 cri
Gwamnatin Morocco, ta ce ta dakile yunkuri 54,000, na bakin haure dake son shiga kasar don tsallakawa Turai, a cikin watanni 8 na farkon bana.

Kakakin gwamnatin kasar Mustapha El Khalifa, ya sanar yayin wani taron manema labarai cewa, adadin ya nuna irin namijin kokarin da hukumomin Morocco ke yi na yaki da kwararar bakin haure.

Ya ce adadin yunkurin bakin haure na shiga kasar tsakanin watan Junairu da Agustan 2017 ya tsaya kan 39,000.

A cewarsa, adadin bakin hauren Morroco, shi ne kaso 13 na jimilar adadin yunkurin kwararar bakin haure da aka bankado a karshen watan Augusta, wanda ya yi kasa da kaso 20 na shekara guda da ta gabata.

Ya ce hukumomin kasar za su ci gaba da kokarin datse hanyoyin kwarara da fasa kaurin bakin haure. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China