in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tesa keyar bakin haure 154 daga Libya zuwa kasar Ivory Coast
2018-08-12 15:26:48 cri
Hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa (IOM) ta sanar a jiya Asabar cewa kimanin bakin haure 154 ne suka amince bisa radin kansu a kwashe su daga Libya zuwa kasarsu ta ainihi Ivory Coast.

Hukumar ta IOM ta fada cikin wata sanarwa cewa zata tabbatar da biyan muradun bakin hauren 154 cikinsu har da yara kanana 6, wajen ba su kariya gabanin a kwashe su zuwa kasar ta Ivory Coast.

Sashen yaki da bakin haure na hukumar ya kuma tabbatar da cewa, an kwashe wasu bakin hauren 'yan kasar Algeria 10 inda aka mayar da su kasarsu ta ainihi a ranar Asabar.

Sama da bakin hauren 10,000 ne suka amince a bisa radin kansu aka mayar da su zuwa kasashen na ainihi daga kasar Libya tun daga farkon wannan shekara, karkashin shirin IOM na mayar da 'yan cin rani kasashensu na ainihi.

Ana fama da cunkoson wuraren zama inda dubban bakin haure ke zama a kasar Libya wadanda aka ceto su a teku ko kuma jami'an tsaron tekun Libya suka damke su.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China