in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojin ruwan Libya sun ceto mutane 57 a gabashin gaabar ruwan kasar, bayan sun yi ba-ta- kashi da masu fasa kauri
2018-09-18 10:33:36 cri
Rundunar sojin ruwan Libya, ta ce ta ceto bakin haure 57 dake cikin kwlae-kwalen roba a gaabar gabashi, bayan sun yi ba-ta-kashi da masu fasa kauri.

Kakakin rundunar Ayob Qassem, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an gudanar da aikin ceton ne da yammacin ranar Lahadi, a yankin dake da nisan kilomita 97 daga birnin Zuwara.

Ayob Qassem ya ce dukkan mutanen da aka ceto 'yan Afrika ne, galibinsu 'yan Nijeriya.

Ya kara da cewa, wani ayarin mutane 6 dake cikin karamin jirgin ruwa ya yi kokarin dakatar da aikin ceton a lokacin da kwale-kwalen sojin ya tunkari wajen, sai dai, sojojin sun yi dauki-ba-dadi da mutanen dake dauke da makamasi, al'amarin da ya tilasta musu tserewa zuwa gaabar Zuwara, wanda ke da nisan kilomita 120 daga birnin Tripoli. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China