in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bakin haure sama da dubu dari shida ne ke makale a Libya
2018-10-08 10:41:22 cri
Hukumar kula da kaura ta duniya ta ce, a halin yanzu akwai bakin haure sama da dubu dari shida dake makale a cikin kasar Libya.

Wata sanarwar da ofishin hukumar dake birnin Tripolin Libya ya fitar, ta ce, bisa alkaluman watannin Yuli da Agustan bana da aka bayar, akwai bakin haure sama da dubu dari shida daga kasashe da yankuna 41 wadanda ke makale a Libya, akasarinsu 'yan kasashen Nijar da Masar da Chadi da Sudan da kuma Najeriya.

Sanarwar ta kuma ce, hukumar kula da kaura ta duniya na hadin-gwiwa da gwamnatin kasar Libya, a wani kokari na mayar da bakin hauren kasashensu bisa radin kansu. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China