in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta bayyana kyakkywar alakarta da kasar Sin a matsayin abun misali ga duniya
2018-10-19 11:18:05 cri
Sudan ta yabawa irin kyakkyawar dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, tana mai bayyana ta a matsayin abun misali ga duniya.

Mataimakin shugaban kasar Sudan kan dangantakar kasar da kasar Sin Awad Ahmed Al-Jaz, shi ne ya bayyana hakan yayin bikin ban kwana ga tawaga ta 33 na jami'an kiwon lafiya Sinawa da suka kammala aikinsu a kasar.

Ofishin Jakadancin kasar Sin a Sudan ne ya shirya bikin, wanda ya samu halartar Minsitan kula da harkokin gwamnatin kasar Ahmed Saad Omer da Jakadan kasar Sin Li Lianhe.

Awad Al Jaz, ya bukaci jami'an lafiya na kasar, su yi amfani da gogewar da suka samu daga takwarorinsu na kasar Sin, kuma su ci gaba da tuntubar juna.

A nasa bangaren, Ahmed Saad Omer, ya yabawa kokarin da kasar Sin ke ba Sudan a dukkan fannoni, yana mai cewa Sin ta samar da gagarumin taimako ga bangarorin tattalin arzki da kiwon lafiya da siyasa na Sudan, a don haka suke gode mata.

Shi kuwa Jakadan kasar Sin, jadadda kudurin kasarsa ya yi na ci gaba da taimakawa Sudan da kuma habaka dangantakarsu.

Kasar Sin ta fara tura jami'an kiwon lafiya zuwa Sudan ne tun a shekarar 1974, domin kula da lafiyar al'ummar kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China