in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan na daukar matakan kawo karshen matsalar kudade a bankuna
2018-10-11 10:18:41 cri
Firaministan kasar Sudan, kuma ministan kudin kasar Mutaz Mussa, ya ce gwamnati na daukar matakan duk da suka wajaba, na wadata bankuna, da na'urorin cire kudi ko ATM da isassun kudade domin biyan bukatun 'yan kasar. Hakan dai ya biyo bayan karancin kudade da ake fuskanta a cibiyoyin kudin kasar a baya bayan nan.

Mussa, wanda ya tabbatar da hakan ta sakon da ya wallafa a shafin sa na Twitter, ya ce ya samu tabbaci daga gwamnan babban bankin kasar Mohammed Khair al-Zubair, cewa ba da jimawa ba za a samar da isassun kudade ga na'urorin ATM wadanda ke sassan kasar, nan da zuwa ranar Asabar mai zuwa.

Tun dai daga watan Fabarairun wannan shekarara ne, aka fara fuskantar karancin kudaden kasar, da ma sauran kudaden musaya na kasashen waje a kasar, sakamakon faduwar darajar kudin kasar a kan dalar Amurka.

Kasar Sudan dai na fuskantar matsalar tattalin arziki, tun bayan samun 'yancin kan Sudan ta Kudu a shekarar 2011, matakin da ya sanya Sudan din rasa kusan kaso 70 bisa dari, na kudaden shigar da take samu daga albarkatun mai. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China