in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru na kasashen Sin da Sudan za su inganta noman auduga a Sudan
2018-09-24 15:05:21 cri
Kwarraru kan harkokin noma na kasashen Sin da Sudan, sun gudanar da wani taron karawa juna sani jiya a Khartoum, babban birnin Sudan, da nufin inganta noma da samar da irin auduga a kasar dake gabashin Afrika.

Taron wanda cibiyar tallafawa fasahohin aikin gona ta kasar Sin ta shirya da hadin gwiwar cibiyar bincike kan harkokin noma ta ma'aikatar kula da ayyukan gona da dazuka ta Sudan, na da nufin inganta amfani da fasahohin da bunkasa noman auduga a Sudan.

Yayin taron, Zhang Lei, kwararre kan harkar noman auduga na kasar Sin, ya jaddada muhimmancin dake tattare da gudanar da binciken kimiyya da amfani da fasahohin zamani wajen inganta noman auduga.

A nasa bangaren, Badr-Eddin Al-Sheikh, mataimakin babban sakataren ma'aikatar kula da ayyukan gona da dazuka ta Sudan, yabawa ya yi da hadin gwiwar dake tsakanin cibiyar ta kasar Sin da cibiyar binciken ta Sudan.

Shi kuwa darekta-janar na cibiyar ta Sudan Abubakr Hussein, bayyana godiya ya yi ga gwamnati da al'ummar kasar Sin, bisa taimakon da suke ba bangarorin tattalin arziki da aikin noma na kasar.

Ya kuma godewa gwamnatin kasar Sin da ta zabo ayarin kwararru da za su bada gudunmuwa a kimiyyance ga bangaren aikin noma da kuma aiwatar da noman auduga a kasar.

Tuni cibiyar ta kasar Sin ta yi nasarar fara amfani da sabon irin auduga mai inganci na kasar Sin a yankin Al-Faw na jihar Al Qadarif dake da nisan kilomita 260 daga kudu maso gabashin Khartoum, domin inganta samar da audugar.(Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China