An dai rantsar da jami'an ne a jiya Litinin, bayan da a ranar Lahadi, jagorancin jam'iyyar NCP mai mulki, ya amince da kudurin shugaban kasar na rushe gwamnatin hadin kan kasa da zabar sabon firaminista, a wani mataki na warware kalubalen tattalin arziki dake addabar kasa.
Gabanin hakan sai da jagororin jami'iyyar ta NCP karkashin jagorancin shugaba al-Bashir suka gana da juna, inda suka tattauna game da bukatar gudanar da sauye sauye ga gwamnatin kasar, tare da gabatar da sunayen wadanda suka cancanta a nada a matsayin sabbin mambobin majalissar zartaswar kasar.
Yayin zaman ne kuma aka amince da nada Mr. Saleh a mataimakin shugaban kasa na farko kadai, bayan da a baya ya taba rike mukamin firaminista da mataimakin shugaban kasa baki daya. Sai kuma Mussa, wanda aka amince da nadin sa a matsayin firaminista, wanda a baya shi ne ministan ma'aikatar noman rani da makamashin lantarki. Kaza lika an amince da nadin Kibir a matsayin mataimakin shugaban kasa na biyu, inda ya maye gurbin Hassabo Mohamed Abdul-Rahman. (Saminu Alhassan)