in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta jaddada kudurinta na kai kayakin agajin yankunan dake hannun 'yan tawaye
2018-10-09 10:18:32 cri
Gwamnatin Sudan, ta jaddada kudurinta na aiki da MDD wajen kai kayakin jin kai yankunan dake hannun 'yan tawaye.

A makon da ya gabata ne, Gwamnatin Sudan ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da MDD, ta tura agajin jin kai da gudanar da gangamin riga kafi a yankunan dake hannun 'yan tawayen SPLM na yankin arewacin kasar, dake Blue Nile da kudancin Kordofan.

Wata sanarwa da Ministan lafiya na kasar Mohamed Abu Zaid Mustafa ya fitar, ta ce a shirye gwamnatin kasar take ta yi aiki da MDD wajen aiwatar da yarjejeniyar.

Ya kuma bukaci kungiyar SPLM ta yankin arewacin, ta ba muradun mazauna yankin muhimmaci, ta amince da tsarin MDD, ya na mai jaddada cewa ma'aikatarsa za ta saukaka hanyoyin aiwatar da gangamin.

Har ila yau, ya yabawa dimbin kokarin da MDD ke yi na kai agajin jin kai, ta hanyar hadin gwiwa da gwmnatin, wadda hukumar kula da agajin jin kai ta kasar ke wakilta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China