in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ya rusa majalisar ministocin kasar
2018-09-10 12:59:56 cri
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir a jiya Lahadi ya yanke shawarar rusa majalisar zartarwar kasar kana ya rage adadin ma'aikatun gwammatinsa, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar SUNA ya rawaito.

SUNA ya jiyo shugaban al-Bashir yana cewa, manufar rage ma'aikatun kasar shine domin rage kashe kudaden gwamnati da kuma tabbatar da inganci a tsarin aikin gwamnati domin sauke nauyin da aka dorawa gwamnatin kasar.

Ana saran za'a rage ma'aikatun gwamnatin kasar daga 31 zuwa 21.

Al-Bashir ya kara da cewa, matakin zai taimaka wajen cimma nasarar aiwatar da manufofin gwamnati wajen biyan muradun jama'ar kasar ta Sudan.

Ana saran matakin zai fara aiki ne bayan amincewar da shugabancin jam'iyyar mai mulkin kasar ta yi a yammacin ranar Lahadi bayan taron da ta gudanar.

Sudan ta fada cikin rikicin tattalin arziki ne tun bayan fuskantar karancin yawan jari da faduwar darajar kudin musayar kasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China