in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Habasha da Eritrea sun bayyana kudurin inganta dangantakar kasashensu
2018-09-18 10:14:25 cri
Firaministan Habasha Abiy Ahmed, da shugaban Eritrea Isias Afwerki, sun jadadda kudurinsu na tabbatar da dorewar yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru 20 ana yi tsakanin kasashen 2 dake gabashin Afrika.

Shugabannin 2 sun bayyana kudurin ne lokacin da suka gana a Saudiyya, ranar Lahadin da ta gabata, domin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta Jidda.

Shugabannin sun gana tare da rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar ne domin kara inganta huldar da suka fara a baya-bayan nan, da ta biyo bayan wasu shirye shirye domin kyautata alakarsu.

Yayin da ake kara zurfafa dangantaka, shugabannin biyu sun yi bikin murnar ranar sabuwar shekarar gargajiya ta kasashen biyu a ranar 11 ga watan nan, tare da sojojin kasashen biyu dake yankunan iyakokinsu.

A ranar 6 ga wata ne Habasha ta bude ofishin Jakadancinta dake Asmara, bayan Eritrea ta bude na ta ofishin dake Addis Ababa a ranar 16 ga watan Yuli.

Ana ganin ci gaban da aka samu a baya-bayan nan a matsayin wani sabon babi ga kasashen biyu, tun bayan yakin da suka tafka daga 1998 zuwa 2000, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 70,000 daga bangarorin biyu.

Yakin ya zo karshe ne a watan Disemban 2000, sanadiyyar yarjejniyar zaman lafiya ta Algiers, sai dai kuma kasashen ba sa jituwa.

Yayin da hulda ke kyautatuwa tsakaninsu, an dawo da layukan wayar sadarwa da zirga-zirga jiragen saman kasashen a tsakanin biranensu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China