in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Habasha ya kaddamar da yankin masana'antun da Sin ta gina
2018-10-08 10:18:09 cri
Firaministan Habasha Abiy Ahmed, ya kaddamar da yankin masana'antu na Adama, wanda ke da nisan kilomita 74 daga kudu maso gabashin Addis Ababa, babban birnin kasar.

Yankin wanda kamfanin gine-gine na kasar Sin ya gina, wani bangare ne na katafaren shirin gwamnatin Habasha na sauya tsarin tattalin arzkin kasar daga dogara kan ayyukan gona, zuwa na ayyukan masana'atu, ya zuwa shekarar 2025.

Ana sa ran yankin masana'antu na Adama da ya mamaye kadada 100, wanda kuma aka gina kan kudi dala miliyan 146, ya samar da guraben aikin yi ga jama'ar kasar kusan 25,000.

Yankin da aka tsara tare da ginawa bisa mizanin kasashen waje, na kunshe da gine-ginen da suka hada da dakin shan magani da na kwana-kwana da bandakuna da wuraren cin abinci da ma na baje koli.

Yayin bikin kaddamarwar, Firaminista Abiy Ahmed, ya ce kaddamar da yankin masana'antu na Adama, na da mutukar muhimmaci wajen biyan bukatun kasar ta fuskar masana'atu da samar da ayyukan yi da kuma inganta kwarewar 'yan kasar da suka kammala karatun gaba da sakandare. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China