in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD ya nuna damuwa game da mutanen da ambaliyar ruwa ta hallaka a Najeriya
2018-10-12 09:56:55 cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya bayyana a jiya Alhamis cewa ya damu matuka sakamakon rahoton da ya samu dake cewa mutane 200 ne ambaliyar ruwa ta hallaka a Najeriya.

Babban magatakardan ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda ibtila'in ya rutsa dasu da kuma jajantawa gwamanti da al'ummar Najeriya, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka samu raunuka, kamar yadda kakakin sakataren MDDr ya fada cikin wata sanarwa.

Sanarwar tace, MDD ta nuna goyon bayanta ga Najeriya game da wannan hali na damuwa kuma a shirye take ta taimakawa kasar idan bukatar hakan ta taso.

Baya ga yawan mutanen da suka rasu, akwai wasu mutanen kimanin 1,300 wadanda aka bada rahoton sun samu raunuka kuma kusan mutane miliyan 2 ne matsalar ambaliyar ruwan ta baya bayan nan ta shafa a yankunan dake kusa da kogin Naija da Benue a Najeriyar. Sama da mutane rabin miliyan ne suka kauracewa matsugunansu kana sama da mutane 350,000 ne suke cikin halin bukatar tallafin gaggawa a sanadiyyar bala'in ambaliyar ruwan a sassan kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China