in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya yi kira da a sabunta dangantakar abota tsakanin Sin da Netherlands
2018-10-15 10:19:19 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira da a sabunta dangantakar abota tsakanin kasarsa da Netherlands, a lokacin da ya isa kasar a jiya domin ziyarar aiki.

Wannan ne karon farko cikin shekaru 14 da firaministan kasar Sin ya kai ziyara kasar.

Wata mukala da jaridar Nouvelles D'Europe ta wallafa a jiya, ta ruwaito Li Keqiang na cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu karkashin wani sabon zagaye na manufarta ta bude kofa da gyare-gyare, ya samar da sabbin damarmakin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Game da yanayin kasuwanci na kasar Sin kuwa, firaministan ya ce, kasar za ta sa kaimi tare da daukar matakan gaggawa na inganta shi, baya ga fadadawa masu zuba jari na kasashen waje hanyoyin shiga kasuwanni da kare hakkin mallakar fasaha.

Ya kara da cewa, wannan kuduri ne da kasar Sin ta dauka, ba don duniya kadai ba, har ma da kara bunkasa ci gabanta, yana mai cewa, za su ci gaba da jajircewa kan wadannan manufofi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China