Bayan ya saurari jawaban da masu masana'antu suka bayar bi da bi, Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta samar da karin damamaki ga baki 'yan kasuwa wadanda suke da shirin zuba jari a kasar, sannan za ta kara sassauta sharudan shigar da su kasuwar kasar Sin. Dukkan masana'antun da za su yi rajista a kasar Sin, za su samu matsayi iri daya da na masana'antun kasar. Bugu da kari, kasar Sin za ta dauki kwararan matakan kare ikon mallakar fasaha, kana ba za a amince da tilastawa wani mika fasaharsa zuwa ga wani daban ba.
Bayan taron, Li Keqiang da Mark Rutte sun halarci wani bikin kulla wasu yarjejeniyoyin hadin gwiwa tsakanin masana'antu da kamfanonin kasashen biyu. (Sanusi Chen)