Li Keqiang ya bayyana cewa, halin rashin tabbas da ake ciki yanzu a duniya na cike da sarkakiya, amma tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa da bude kofa tare da hadin gwiwa, hanzu yanzu, su ne manyan jigon dake kasancewa a wannan zamanin. Ya ce ya kamata nahiyoyin Asiya da Turai, wadanda suke kasancewa muhimman karfi ga kokarin ci gaban tattalin arziki da tabbatar da kwanciyar hankalin duniya, su kara yin mu'amala da hadin gwiwa, ta yadda za su iya yin kokarin tabbatar da zaman lafiya da shawo kan kalubale tare domin neman ci gaba na bai daya.
Li Keqiang ya isa Brussels bayan da ya kawo karshen ziyararsa a hukumance a kasar Holland. (Sanusi Chen)