in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin da Netherlands sun yi kira da gudanar da cinikayya cikin 'yanci
2018-10-16 10:32:03 cri

Kasashen Sin da Netherlands sun yi kira ga kasashen duniya da su inganta tsarin cinikayya cikin 'yanci da kare huldar kasa da kasa, domin magance kalubale na bai daya dake tunkarar duniya.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa tare da firaministan Netherlands Mark Rutte, firaministan Sin Li Keqiang dake ziyara a kasar, ya ce kasashen biyu za su cimma matsaya da yin aiki tare, domin bunkasa cinikayya cikin 'yanci da kuma kara inganta tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa domin magance yanayin rashin tabbas dake karuwa.

Ya ce ciniki cikin 'yanci ba ya nufin watsi da ciniki cikin adalci, inda ya yi bayanin cewa, idan ba a cinikayya cikin 'yanci, to ba zai yuwu a samu adalci ba, haka zalika idan babu adalci, cinikayya cikin 'yanci ba za ta samu ci gaba mai dorewa ba.

A bangaren huldar kasa da kasa kuwa, Li Keqian ya ce wannan ba ya nufin raina dangantakar kasa da kasa, sai dai inganta demurokadiyar tsarin siyasar duniya.

Firaministan na Sin, ya kuma jaddada kudurin kasarsa na kara bude kofa ga kasashen duniya, yana mai cewa kasarsa za ta ci gaba da fadada kasuwarta ga jarin Netherlands a fannonin bada hidima da na aikin gona.

A nasa bangaren, Mark Rutte, ya ce manyan kasashe kan yi aiki tare, kuma a bayyane, bisa adalci da tsarin cinikayyar kasa da kasa, yana mai cewa kasarsa da Sin za su hada gwiwa wajen tunkarar kalubalen da duniya ke fuskanta.

Da yake yabawa nasarar hadin gwiwar kasashen 2 a fannoni daban-daban da hadin gwiwar da suke yi wajen magance kalubalen da suka hada da sauyin yanayi, Mark Rutte ya ce Netherlands za ta hada hannu da kasar Sin wajen bunkasa dagantaka da hadin gwiwarsu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China