in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya yi kira da a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin mambobin kungiyar SCO
2018-10-13 15:53:06 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bukaci kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO, su kara karfafa hadin gwiwa irin ta moriyar juna a fannoni daban-daban, tare da samun ci gaba na bai daya.

Da yake jawabi ga taron majalisar shugabanni kasashen kungiyar na 17, a Dushanbe babban birnin Tajikistan, Li Keqiang, ya bayyana bangarorin da kasashen ke hadin gwiwa da suka hada da tattalin arziki da cinikayya da sadarwa da sarrafa kayayyaki.

Ya ce, yayin taron kungiyar da aka yi a farkon shekarar nan a birnin Qingdao na kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran shugabannin kungiyar, sun cimma muhimmiyar matsaya tare da kara kaimi ga makomar kungiyar.

Domin samun dorewar ci gaba, Li Keqiang ya gabatar da shirin karfafa hadin gwiwa a fannonin da suka hada da tsaro da tattalin arziki da cinikayya da sarrafa kayakki da sadarwa da kirkire-kirkire da dangatakar jama'ar kasashen.

Da yake tsokaci da game da koma bayan tattalin arzikin duniya da na cinikayya tsakanin kasa da kasa, Li ya ce mambobin kungiyar na fuskantar sabbin kalubale ta fuskar ci gaban tattalin arziki.

Ya kuma yi kira ga mambobin kungiyar, su mara baya ga cinikayya cikin 'yanci bisa tsari da ka'idojin cinikayya na kasa da kasa da bunkasa cinikayya da zuba jari cikin 'yanci da sauki.

Firaministoci da wakilai mahalarta taron, sun ce bisa halin da ake ciki yanzu, kasashen na bukatar hadin kai da zaman lafiya da tabbatar da 'yancin cinikayya da zuba jari da kare huldar kasa da kasa.

Sun kuma amince su aiwatar da sakamakon taron da suka yi a Qingdao, tare da karfafa hadin gwiwa a fannonin cinikayya da zuba jari da makamashi da aikin gona da musaya tsakanin jama'arsu da hada hannu wajen yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China