in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya isa Tajikistan don halartar taron SCO da kai ziyarar aiki
2018-10-11 19:48:09 cri

A yau Alhamis ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa kasar Tajikistan don halartar taron shekara-shekara na shugabannin kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice tare da kai ziyarar aiki a kasar.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta rabawa manema labarai gabanin ziyarar firaministar na Sin ta nuna cewa, yayin taron na SCO karo 17, firaminista Li zai tattauna da sauran shugabanni kan wasu batutuwa kamar kara zage damtse wajen gina shawarar ziri daya da hanya daya da karfafa alaka a fannonin cinikayya da hada kasashen kungiyar da musaya tsakanin al'ummomin kasashen, ta yadda za a zurfafa alaka tsakanin kasashe mambobin kungiyar a dukkan fannoni.

Sanarwar da kara da cewa, ana sa ran Li zai yi kira da a nuna adawa da ra'ayi na kashin kai da ba da kariya ga harkokin cinikayya, da gina tsarin tattalin arzikin duniya da kowa zai yi na'am da shi da gina al'umma mai kyakkayawar makoma ga kungiyar ta SCO.

Ana kuma sa ran fitar da sanarwar bayan taro ta hadin gwiwa, wadda za ta yi magana da murya guda kan manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya. Za kuma a sanya hannu kan muhimman takardu na hadin gwiwa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China