Firaministan zai kuma gana da shugabannin Tajikistan da Netherlands, bayan haka zai halarci taron hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Turai na ASEM karo na 12, wanda zai gudana a birnin Brussels, yayin da zai gudanar da ziyara a kasar ta Belgium.
Firaministan na Sin zai gudanar da wannan ziyara ne bisa gayyatar firaministan Tajikistan Kohir Rasulzoda, da na Netherlands Mark Rutte, da na Belgian Charles Michel. Sauran su ne shugaban majalissar Turai Donald Tusk, da shugaban hukumar zartaswar kungiyar Jean-Claude Juncker. (Saminu Hassan)