Yayin zaben fidda gwani da aka gudanar a daren ranar Asabar, Atiku Abubakar ya doke sauran 'yan takara 11, ciki hadda shugaban majalissar dattawan Najeriya Bukola Saraki, da gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal.
Atiku ya lashe zaben fidda gwanin ne da kuri'u 1,532, wato kusan rabin jimillar kuri'un da aka kada gaba daya, a zaben na birnin Patakwal din jihar Rivers.
Atiku ya rike mukamin mataimakin shugaban Najeriya, tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007, ya kuma taba kasancewa daya daga cikin masu marawa gwamnatin dake kan mulki ta shugaban Muhammadu Buhari baya. To sai dai kuma daga baya ya fara sukar gwamnatin mai ci, bayan da ya fice daga jam'iyya mai mulki ta APC cikin shekarar da ta gabata, ya kuma koma jam'iyyar adawa ta PDP. (Saminu Alhassan)