in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude baje koli mafi girma na kasar Sin a birnin Guangzhou
2018-10-15 20:00:19 cri
Da safiyar yau Litinin ne aka bude baje koli mafi girma a kasar Sin a birnin Guangzhou, fadar mulkin lardin Guangdong, baje kolin dake tattaro masu ruwa da tsaki, da kamfanoni, akasari masu hada hadar shigo da kayayyaki.

Ana dai gudanar da wannan baje koli ne a duk shekara, a makamancin wannan lokaci na kaka a birnin na Guangzhou. Baje kolin hajojin da ake shigo da su, da wadanda ake fitarwa, wanda aka fi sani da "Canton Fair", na matsayin wani mizani na awon ci gaban hada hadar cinikayyar waje ta kasar Sin.

Da yake tsokaci yayin bikin bude baje kolin, kakakin hukumar gudanawar sa Xu Bing, ya ce batun hajojin da ake shigo da su daga waje, shi ne ginshikin baje kolin na bana, kasancewar yanzu kasar Sin na kara mai da hankali ga kara bude kasuwanninta na cikin gida, ga 'yan kasuwa daga ketare. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China