in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kaddamar da kwamitin kasa da kasa na kwararru domin warware sabanin cinikayya
2018-08-27 09:53:17 cri
Babbar kotun al'umma ta Sin SPC, ta kaddamar da kwamitin kasa da kasa na kwararru ko ICEC, domin warware sabanin cinikayya, kwamitin da ke da alhakin tallafawa wajen shiga tsakani, da aiwatar da sulhu ko shari'a a fannin cinikayya da ta shafi kasa da kasa.

Kwamitin da aka kaddamar a jiya Lahadi, na kunshe da mambobi 32, wadanda suka hada da Sinawa, da kuma kwararru daga kasashen waje. Kaza lika zai rika aiki da hadin gwiwar sauran kotunan kasa da kasa, ta yadda zai ba da gudummawar warware korafe korafe, wadanda suka shafi hada hadar cinikayya.

An dai zabo mambobin sa ne daga sassan fannin shari'a daban daban, kuma rukunin farko na mambobin sa sun kunshi jagororin kungiyoyin duniya, da kwararru a fannin shari'a da masana, da gogaggun masu shari'a da lauyoyi.

Kotun SPC ta kafa kotunan kasa da kasa guda biyu na farko a birnin Shenzhen dake lardin Guangdong, da birnin Xi'an dake Shaanxi a ranar 29 ga watan Yunin da ya gabata.

Ana sa ran fitar da hotuna, da takardun bayanai game da kwarewar aikin mambobin kwamitin, a shafin yanar gizon kotun hada hadar cinikayya ta kasa da kasa da yaren Sinanci da kuma Turanci.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China