Yayin wani taron manema labarai da ya kira a jiya, kakakin ma'aikatar Gao Feng, ya ce kasar Sin za ta yi amfani da kalubalen wajen kara ingantawa da bunkasa tsarin tattalin arzikinta, tare da samar da ci gaba mai inganci.
Ya ce kasar Sin ta kasa tantance ainihin dalilan da suka sanya Amurka bullo da sabbin halayya, kuma Sin din ba ta goyon bayan sanya siyasa cikin harkokin tattalin arziki da cinikayya ba. Ya ce kofar kasar a bude take don tattauna yadda za a warware batun da Amurka, amma dole ne tattaunawar ta kasance bisa gaskiya da adalci da cika alkawurrra.
Ya ce yuwuwar tattaunawar da kuma lokacin da za a yi, za su dogara ne kan Amurka.
Gao Feng ya ce ya kamata Amurka ta fahimci yanayin sosai, sannan kada ta raina batun warware rikicin da yakini da kuma karfin kasar Sin.
Har ila yau, ya ce suna fatan za a warware takaddamar cinikayya da tattalin arziki dake tsakanin kasashen biyu, amma kuma sun shiryawa duk wani abu da- ka-je-ya-zo. (Fa'iza Mustapha)