in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa
2018-08-31 10:56:14 cri
Kakakin ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, Gao Feng, ya ce ba tare da la'akari da matsi daga Amurka ba, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufar gyare gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, tare da ci gaba da aiki da sauran kasashe wajen kare tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa.

Da yake mayar da martani game da zargin rashin adalci a harkokin cinikayyar kasar Sin da Amurka ta yi, Gao Feng ya ce kasar Sin na gudanar da harkokin cinikayya a kasashen waje ne bisa kiyaye ka'idojin hukumar kula da cinikayya ta duniya.

Ya kara da cewa, hadin gwiwar cinikayya tsakanin Sin da Amurka wanda ke da tsari irin na moriyar juna, ya bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen, tare da amfanawa al'umominsu.

A wani taron sauraron ra'ayin jama'a da ofishin wakilan cinikayyar Amurka ya gudanar a baya-bayan nan game da sanya harajin kan kayakin kasar Sin da darajarsu ta kai kusan dala biliyan 200, sama da kaso 90 na mahalarta taron sun nuna rashin goyon bayansu ga matakin. A cewar Gao Feng, wannan ya nuna cewa matakin da Amurka ta dauka bisa radin kanta, ya sabawa muradun al'umma.

Kakakin ya kuma bayyana yakini game da ci gaban cinikayyar kasar Sin da kasashen ketare, domin kasar za ta ci gaba da saukaka harkokin cinikayya da bullo da sabbhin matakan kare hakkokin 'yan kasuwa, ciki har da na kamfanoni baki dake kasar, kamar dai yadda ka'idojin WTO suka tanada.

Har ila yau, ya ce kasar Sin za ta tabbatar nasarar baje kolin kayakin da ake shigowa da su daga ketare, tare da fadada kayakin domin cimma bukatun jama'a da na kamfanonin cikin gida. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China