Kasar Sin na kara yin kwaskwarima kan yankunan cinikayya cikin 'yanci
Kwamitin zurfafa yin kwaskwarima a dukkan fannoni na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, ya zartas da takardu guda 6 a kwanakin baya, ciki har da takardar jerin matakai game da goyon bayan yankunan cinikayya cikin 'yanci wajen zurfafa yin kwaskwarima da kirekire-kirkire, wadda ta fi sauran takardun jan hankulan jama'a. Ko da yake ba a sanar da wasu abubuwa da yawa dake cikin takardar ba, amma takardar ta bayyana niyyar gwamnatin kasar Sin ta zurfafa yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen ketare a fannin. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku