in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na goyon bayan sake fasalin WTO, amma ba kirkiro sabuwar hukuma ba
2018-09-28 10:09:55 cri
Ma'aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin, ta ce ta na goyon bayan sake fasalin hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO), wanda zai daukaka ka'idojinta, amma ba zai kirkiro sabuwar hukuma ba.

Kakakin ma'aikatar Gao Feng, wanda ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da ya gudana jiya, ya ce hukumar na fuskantar kalubale game da ikon da take da shi da ingancin ayyuka, a lokacin da ake fama da kariyar cinikayya da ra'ayi na kashin kai, yana mai cewa akwai bukatar sake fasalinta domin inganta tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa, ta yadda zai dace da zamani.

Ya ce duk da kalubalen, tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa karkashin jagorancin WTO, ya taimaka gaya, wajen yaki da kariyar cinikayya tare da inganta cinikayyar, kana ya samar da ci gaba mai dorewa.

Gao Feng ya ce bai kamata sake fasalin ya sauya ka'idojin hukumar ba, ko kuma mayar da hannun agogo baya game da batun 'yancin cinikayya.

Bugu da kari, ya ce tilas ne tabbatar da sauyin bai kirkiro sabuwar hukuma ba, yana mai cewa kasar Sin na adawa da duk wani yunkuri na wata mambar hukumar na kakabawa sauran mambobi muradunta na kashin kai. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China