Alex Akpa, mai rikon mukamin babban daraktan hukumar bunkasa kimiyyar tsirrai ta kasar (NABDA) ya fada a Abuja babban birnin kasar cewa, wannan yunkuri ya zama tilas domin cike wagagen gibin da kasar ke da shi na bukatar makamashi.
Akpa, ya bada wannan sanarwa ne a lokacin taron musayar ra'ayoyi game da lalibo damammakin zuba jari a fannin kimiyyar tsirrai da bunkasa ci gaban makamashi ta hanyar tsirrai.
Daraktan ya shedawa mahalarta taron cewa, Najeriya za ta kara zurfafa kokarinta ta hanyar gudanar da bincike kan kimiyyar tsirrai tare da bunkasa ci gaban makamashi ta hanyar tsirrai a kasar.
Ya kara da cewa hukumar ta NABDA ita ce ke da alhakin bunkasa ci gaban kimiyyar tsirrai a Najeriyar, kuma hukumar tana da cibiyoyi 30 a duk fadin kasar. (Ahmad Fagam)