Ministan wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, yayin zantawar sa da wakilan manoma, ya ce za a iya kaucewa wannan matsala ne kawai, idan aka hanzarta sake shuka sabon iri a gonaki.
Ambaliyar ruwa ta shafi jihohi da dama dake samar da mafi yawan shinkafar da ake nomawa a Najeriya. To sai dai kuma ministan ya ce gwamnati na duba hanyar da za ta bi, domin tallafawa manoman da ambaliyar ruwar ta shafa.
Kaza lika ministan ya ce akwai irin shinkafa da ake samarwa a cibiyar bunkasa irrai ta kasa masu jure ambaliyar ruwa, kamar faro 66, da 67. Don haka ma'aikatar noma ta kasar na fatan gabatarwa manoma irin wadannan nau'o'i na irran shuka a wadace, domin amfani da su a nan gaba. (Saminu Hassan)