in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararrun MDD sun bukaci a kawo karshen muzgunawa yara mata a fadin duniya
2018-10-10 10:30:10 cri
Gungun kwararrun masana hakkin dan adam na MDD sun bakaci kasa da kasa da su dauki kwararan matakai don kawo karshen muzgunawa da nuna wariya da kuma cin zarafi da yara mata ke fuskanta a sassan duniya.

A sanarwar hadin gwiwa da suka fitar domin tunawa da zagayowar ranar yara mata ta kasa da kasa, wanda aka ware ranar 11 ga watan Oktoban kowace shekarar, kwararrun masanan sun bayyana cewa, akwai bukatar a dauki matakan da suka dace domin baiwa yara mata cikakkiyar dama domin su shiga a dama da su a dukkan harkoki na rayuwa.

A cewar kwararrun, har yanzu yara mata ba su kubuta ba daga fuskantar cin zarafi kuma da dama daga cikinsu sun sha gamuwa da matsalolin yin safararsu, da keta musu haddi ta hanyar fyade da tilasta musu yin auren dole, da bautar da su, da tilasta su yin karuwanci, da tilasta su daukar ciki.

Kwararru sun kuma ce ana tursasawa 'yan mata yin aikace aikace a gidajen 'yan uwansu ba tare da biyansu hakkokinsu ba. Kuma ana yin amfani da su wajen yin aikatau a wasu gidaje tun suna da kananan shekaru domin daukar nauyin iyalansu.

"Mafi yawan kalubalolin da 'yan matan ke fuskanta sun samo asali ne a sakamakon wata dadaddiyar al'ada da mummunan zato da ake nunawa game da rawar da jinsin mata ke takawa inda ake danganta yara matan da su, hakan wani mummunan tasiri ne na al'adu," in ji kwararrun. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China