in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta hada gwiwa da Japan wajen bunkasa huldar da ke tsakaninsu, in ji Li Keqiang
2018-08-12 15:36:35 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce kasar sa a shirye take ta yi hadin gwiwa da Japan, wajen bunkasa kawance na tsawon lokaci, cikin daidaito da ci gaba.

A jiya Lahadi ne dai Li Keqiang, da takwaransa na kasar Japan Shinzo Abe, suka yi musayar sakwannin taya juna murnar cika shekaru 40 da sanya hannu, kan yarjejeniyar zaman lafiya da abota tsakanin kasashen su.

A sakon nasa, Li ya ce cikin shekaru 40 da suka gabata, hulda tsakanin Sin da Japan ta samu tagomashi yadda ya kamata, wadda hakan ta amfana wa al'ummun kasashen biyu, tare da fadada wadata da kwanciyar hankali a yankin da suke, da ma duniya baki daya.

A watan Mayun da ya gabata, firaministan na Sin ya kai ziyara kasar Japan, ya kuma halarci taro na 7 na hadin gwiwar shugabannin Sin, da Japan da Koriya ta kudu.

Li ya ce ziyarar ta sa, ta tallafa wajen mayar da yanayin kawance tsakanin Sin da Japan kan turba madaidaiciya. A cewar sa Sin a shirye take ta yi aiki da Japan wajen kare ginshikin siyasa na sassan biyu, da karfafa hadin gwiwa don cimma moriyar juna, da daidaita duk wani sabani, tare da ingiza ci gaban sassan biyu a tsawon lokaci bisa tushen "waiwaiye adon tafiya da kuma hangen nesa doming gaba".

A nasa sakon kuwa, Abe jinjinawa kwazon kasashen biyu ya yi, yana mai cewa sun cimma gagarumar nasara a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da raya al'adu, da kuma musaya tsakanin al'ummunsu.

Firaminista Abe ya kuma yaba da ziyarar da Mr. Li ya kai kasar sa a watan Mayun da ya shude, yana mai fatan zai ziyarci Sin nan gaba cikin wannan shekara, a wani mataki na kara karfafa alakar sassan biyu, da daga matsayin dangantakar su ya zuwa mataki na gaba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China