Firayin ministan kasar Sin, kuma shugaban karamar kungiyar jagorancin aikin raya tattalin arzikin yankunan dake yammacin kasar ta majalisar gudanarwar kasar Sin Li Keqiang, ya kira wani taro a ranar 21 ga watan nan, domin tsarin hanyar gudanar da aikin yadda ya kamata.
Yayin taron, Li ya bayyana cewa, idan ana son kara karfafa gogayya ta samar da kayayyaki a yankunan dake yammacin kasar, ya dace a kara mai da hankali kan sabon tsarin raya tattalin arziki, kana a kara mai da hankali kan aikin bude kofa na yankunan ga sauran yankunan fadin kasar, da kuma kasashen ketare.
Li ya kara da cewa, abu mafi muhimmanci shi ne a ci gaba da nacewa kan manufar yaki da talauci a yankunan, domin kyautata sharadin rayuwar mazauna wuraren, tare kuma da kara samar da aikin yi ga matasa, da kyautata hidimar inshorar ritaya ga tsofaffi.(Jamila)