in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gana da sakataren harkokin wajen Burtaniya
2018-07-31 20:27:08 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da sakataren harkokin wajen Burtaniya Jeremy Hunt a nan birnin Beijing, inda ya yaba da ci gaban da aka samu a alakar dake tsakanin kasashen biyu da a dukkan fannoni.

Li ya ce, a matsayinsu na mambobin din-din-din a kwamitin tsaron MDD, kana manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, Sin da Burtaniya na da rawar da za su taka wajen tabbatar da ka'idoji da tsarin kasa da kasa kamar yadda manufofi da tsare-tsaren MDD suka tanada, da ma tsarin cinikayyar bangarori daban-daban kamar yadda yake kunshe cikin manufofin kungiyar cinikayya ta duniya.

Mr Li ya yi kira ga bangarorin biyu da su yi kyakkyawan amfani da damammakin juna, da fadada alaka a fannoni daban-daban, kana su yi amfani da damar kasuwar hannayen jari ta Shanghai-London Connect da za a kaddamar cikin wannnan shekara, wajen bullo da matakan ci gaban hadin gwiwa da samun moriya tare.

Hunt, shi ne sakataren harkokin wajen Burtaniya na farko da ya kawo ziyara kasar Sin, ya kuma yaba da ci gaban alakar dake tsakanin kasashen biyu a wannan zamani da muke ciki.

Ya ce, duba da yadda duniya ke fuskantar wani muwayacin hali, ya kamata Sin da Burtaniya su karfafa sadarwa da bude kofar kasancewar bangarori daban-daban, cinikayya cikin 'yanci da kare ka'idojin kasa da kasa kamar yadda doka ta tanada.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China