Shugaba Xi ya ce ya yaba da gudummawar da shugaba Buhari ya bayar wadda ta kai ga samun nasarar taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da aka cimma a birnin Beijing na kasar Sin, da darajanta ci gaban alakar kasashen biyu. Yana kuma fatan hada kai da shugaba Buhari wajen daga matsayin alakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa wani sabon matsayi ta yadda za ta yi amfana al'ummomin kasashen biyu.
Bugu da kari, shugaba Xi ya yi fatan samun kyakkyawar makoma da farin ciki ga Najeriya gami da al'ummominta. (Ibrahim)