in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi da takwaransa na Angola sun tsai da kudurin ciyar da huldar kasashensu gaba
2018-10-09 20:47:07 cri

Yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Angola Manuel Lourenso a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, inda suka yi shawarwari a tsakaninsu.

Xi ya jaddada cewa, kasarsa ta goyi bayan kokarin da al'ummun kasashen duniya suke yi domin nuna adawa da tsoma bakin da sauran kasashen duniya suke yi wa harkokin gidan kasashensu, tare kuma da samun ci gaba yadda ya kamata. Kana yana fatan hada kai tare da kasashen Afirka domin aiwatar da nasarorin da aka cimma yayin taron kolin Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, ban da haka kuma, yana fatan sassan biyu za su kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninsu a fannonin al'adun gargajiya da masana'antu, ta yadda za su samu moriya tare.

A nasa bangare, shugaba Lourenso ya bayyana cewa, dadadden hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Angola ya taimaka ga ci gaban tattalin arzikin kasar, yana fatan sassan biyu za su kara karfafa hadin gwiwa a fannin gina kayayyakin more rayuwar jama'a da inganta rayuwar al'ummar kasar, ta yadda kasar Angola za ta samu ci gaba bisa taimakon kasar Sin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China