Shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma Janar Sakatare na JKS, kana shugaban rundunar sojin kasar, na cikin dimbin jami'an da suka fito don tunawa da mazan jiyan, a jajibirin ranar murnar kafuwar sabuwar kasar Sin.
Sauran manyan jami'an da suka hallara sun hada da Li Keqiang da Li Zhanshu da Wang Yang da Wang Huning da Zhao Leji da Han Zheng da Wang Qishan. (Fa'iza Mustapha)