Da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Kwamishinan kula da harkokin zuba Jari na kasar, Mekuria Belachew, ya ce yankunan 6 da suka dauki ma'aikata 55,000 sun samarwa kasar kudaden da take bukata a cikin shekarar.
Yankunan masana'antun 6 sun hada da Kombolcha da Mekelle da Eastern da Huajian da Hawassa da kuma Modjo.
Kwamishinan ya kara da cewa, ana sa ran Firaministan Habasha Abiy Ahmed, wanda zai kawo ziyara kasar Sin karon farko a makon gobe, don halartar taron dandalin tattaunawar Sin da Afrika, zai ja ra'ayin kamfanonin kasar Sin su zuba jari a bangarorin sarrafa amfanin gona da samar da magunguna na kasar. (Fa'iza Mustapha)