in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Turkiyya, Iran da Rasha sun yi alkawarin hadin gwiwa wajen tunkarar rikicin Syria
2018-04-05 11:56:38 cri
Kasashen Rasha, Turkiyya da kuma Iran sun sha alwashin gaggauta daukar matakan tabbatar da ganin an samu daidaituwar al'amurra don kawo karshe yakin da ake gwabzawa a kasar Syria, kasashen uku sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar bayan kammala taron koli a jiya Laraba.

Sanarwar ta ce, shugabannin kasashe na Turkiyya, Rasha da Iran sun nanata aniyarsu na yin hadin gwiwa domin gaggauta daukar matakan da za su kawo kwanciyar hankali da kuma bada kariya ga fararen hula wadanda rikicin kasar ya daidaita, kana da hanzarta kai dauki ga mutanen dake bukatar daukin gaggawa a yankunan da rikicin ya ta'azzara. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China