in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sham: Matakin soja da Amurka za ta dauka a Sham zai tsananta halin da ake ciki
2018-04-13 16:09:33 cri

Shugaban kasar Sham Bashar Al-Assad, ya sanar a jiya Alhamis cewa, Amurka ta yi ikirarin daukar matakin soja kan kasarsa, abun da ya ce zai tsananta halin da ake ciki a kasar, tare kuma da yin kalubale ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha ya bayyana a wannan rana cewa, yana fatan kasashen yamma masu ruwa da tsaki za su yi hakuri don warware matsalar Sham ta hanyar da ta dace.

Har ila yau a jiya, kasashen yamma masu ruwa da tsaki, sun bayyana ra'ayinsu kan matsalar kasar Sham. Inda shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ce, Faransa ta lashi takobin tinkarar 'yan ta'addan Sham har abada, abun da ya kasance matakin farko da Faransa take dauka wajen warware rikicin kasar Sham. Ban da wanann kuma, gwamnatin kasar Birtaniya ta ce, kamata ya yi a dauki mataki don hana bullowar karin hare-haren makamai masu guba a Sham, game da wannan batu ne kuma ta yi hadin gwiwa da Amurka da Faransa. Sai dai a nata bangaren, shugabar gwamnatin Jamus Angela Dorothea Merkel ta bayyana cewa, Jamus ba za ta shiga cikin matakan soja da wasu kasashen yamma za su dauka nan gaba kan kasar Sham ba, amma ta yi Allah wadai da matakin amfani da makamai masu guba a kasar. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China