Rahoton na IPCC yace, burin da ake da shi na mayar da matakin dumamar yanayin zuwa maki 1.5, maimakon maki 2 da aka bukata a yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, zai haifar da kyakkyawar makoma ga bil adama da muhallain halittu.
Sanarwar da mista Guterres ya fitar tace, rahoton da kwamitin kwararrun masana kimiyyar sauyin yanayi suka bada tamkar sa kaimi ne ga kasa da kasa. Rahoton ya tabbatar da cewa, sauyin yanayi yana matukar karuwa cikin sauri sama da yadda ake tafiyar da harkokin yau da kullum, kuma lokaci yana cigaba da kurewa, inji sanarwar.
Masanan sun nuna girman banbancin dake tsakanin dumamar yanayi na maki 1.5 da maki 2, yace rabin maki na dumamar yanayi zai iya haifar da gagarumin sauyi ga duniya baki daya.
Maki 2 na dumamar yanayi zai iya haifar da matsanancin zafi da zai iya shafar miliyoyin jama'a, wanda zai iya haddasa gagarumar hasara, da matsalar karanci ruwa a sassan duniya daban daban da ake fama da rashin zaman lafiya, da kara girman matsalar a yankunan masu fama da daskarewar kankara inda za'a iya samun narkewar kankarar a lokacin zafi, sannan za'a iya fuskantar barazanar bacewar wasu nau'ikan kyawawan halittu daga doron kasa, inji mista Guterres. (Ahmad Fagam)