in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata tawagar MDD na kan hanyar zuwa DR Congo don duba shirye-shiryen zaben kasar na watan Disamba
2018-10-05 15:30:42 cri
A jiya Alhamis ne mambobin kwamitin sulhun MDD suka tashi zuwa Jamhuriyar demokiradiyar Congo don ganin yadda ake gudanar da shirye-shirye gabanin zabukan kasar na watan Disamba.

Tawagar dai ta kunshi wakilan kasashen Bolivia da Equatorila Guinea da Faransa. Kasar Bolivia ita ce ke rike da shugabancin kwamitin sulhun majalisar na wannan wata, yayin da kasar Faransa ke zama mambar kwamitin da za ta rubuta shawarwari game da Jamhuriyar demokiradiyar Congo.

A ranar Litinin din mako mai zuwa ne ake sa ran tawagar za ta dawo birin New York na kasar Amurka. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China