in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren MDD ya bukaci 'yan kasar Kamaru da su fito su yi zaben shugaban kasa
2018-10-05 15:20:16 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi kira ga daukacin 'yan kasar Kamaru da su fito su kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa ranar Lahadi dake tafe.

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq wanda ya sanar da hakan cikin wata sanarwa, ya ce, babban sakataren MDD ya karfafawa 'yan kasar ta Kamaru gwiwa da su fito yayin da suke shirin zaben shugaban kasa a ranar 7 ga watan Oktoba, domin sauke nauyin da tsarin demokiradiya ya ba su, kana su gudanar da zabe mai inganci cikin lumana wanda kowa zai amince da shi.

Guterres ya kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su kai zuciya nesa kafin da kuma bayan gudanar da zaben. Ya kuma bukaci dukkan 'yan takara da su warware dukkan wasu korafe-korafe da suka shafi zabe ta hanyar doka.

Jami'in na MDD ya kuma yi Allah wadai da duk wata barazanar tashin hankali ko tsaratarwa da wata duk kungiya ke shirin tayarwa, yana mai nanata bukatar warware duk wata rashin fahimta ta hanyar tattaunwa.

Ya kuma nanata kudurin MDD na ba da taimakon da ya dace ta wannan fuska. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China