Uwar Kungiyar kwadago ta kasar, ta yi kira da a gudanar da zanga-zanga a yau Laraba, da nufin nuna adawa da karin harajin da ya haifar da karuwar farashin kayayyaki.
A makon da ya gabata ne Ministan kudi na kasar, Mthuli Ncube, ya sanar da karin, a matsayin wani mataki na samun karin kudin hidimtawa al'umma.
Sai dai akasarin 'yan kasar ba su yi na'am da matakin ba, inda suke ganin dama can suna biyan harajin da wuce kima.
Wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar a jiya, ta ce ba zai yuwu a gudanar da zanga-zangar ba, saboda har yanzu haramta taron jama'a da aka yi biyo bayan barkewar cutar Kwalara a kasar na nan daram.
A don haka, rundunar ta ce ya kamata kungiyar 'yan kwadagon da ta shirya zanga-zangar da sauran rassanta, su yi la'akari da umarnin gwamnati, musammam kan zirga-zirgar jama'a da dama daga wani wuri zuwa wani, ciki har da wuraren da aka samu barkewar cutar kwalara. (Fa'iza Mustapha)