in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Zimbabwe ta ce akwai sabon yakinin ganin bunkasar tattalin arzikin kasar
2018-10-06 16:03:55 cri
Ministan kudin Zimbabwe Mtuli Ncube, ya ce an yi hasashen tattalin arzikin kasar zai karu da kaso 9 a shekarar 2019, sannan ya kai kaso 9.7 a 2020, bisa sabon yakinin kasuwanci a tattalin arzikin.

Da yake kaddamar da sabon daftarin daidaitawa da farfado da tattalin arziki na Transitional Stabilization Program TSP a takaice, Mthuli Ncube ya ce za kuma a gabatar da hanyar bunkasar tattalin arzikin cikin shirin na TSP da zai gudana daga Octoban bana zuwa Disamban 2020, wanda ke da nufin daidaita tsarin tattalin arziki ta hanyar daidaita harkokin kashe kudi da kudin shiga, da ci gaban kayayyakin more rayuwa da bunkasar harkokin fitar da kayayyaki.

An yi hasashen tattalin arzikin Zimbabwe zai karu da kaso 6.3 a bana, adadin da ya zarce kaso 4.5 da aka yi hasashe a baya.

Shirin na TSP shi ne na farko cikin jerin dabarun neman ci gaba cikin wani lokaci da gwamnati za ta aiwatar a kokarinta na sauya Zimbabwe zuwa kasa mai matsakaicin kudin shiga ya zuwa 2030.

Bayan shekarar 2020, gwamnatin za ta kaddamar da wasu dabarun ci gaba guda 2 da za su dauki shekaru 5-5, inda na farkon zai gudana daga 2021 zuwa 2025, yayin da na biyun zai gudana daga 2026 zuwa 2030. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China