in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Zimbabwe ta ce gyara tsarin kawar da najasa ne zai kawo karshen cutar kwalara
2018-09-19 10:28:02 cri
Gwamnatin Zimbabwe, ta ce sake tsarin shimfida bututan ruwa da na kawar da najasa ne hanya mai dorewa ta kare sake barkewar cutar kwalara a kasar.

Cutar da ta barke a birnin Harare, ta kashe mutane 30 inda wasu 5,000 suka kamu da ita. Wannan shi ne karo na 2 da kasar ta fuskanci gagarumar barkewar cutar kwalara tun bayan ta shekarar 2008, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane 4,000.

A farkon wannan watan ne cutar ta barke, kuma kawo yanzu ta bazu zuwa wasu sassan kasar.

Ana alakanta barkewar cutar da fashewar bututun kawar da najasa da ta bata ruwan rijiyoyin burtsatsai.

Majalisar kula da birnin Harare dai ta gaza samar da tsaftaccen ruwan sha cikin wani lokaci, lamarin da tilastawa mazauna yankin dogara da ruwa mara isashiyar tsafta daga rijiyoyi da rijiyoyin burtsatsai. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China