in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon shugaban kasar Zimbabwe
2018-08-27 10:19:47 cri

Babban jojin kasar Zimbabwe Luke Malaba, ya rantsar da Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon shugaban kasar na wa'adin aikinsa na farko, na tsawon shekaru 5.

Da yake shan rantsuwar, Emmerson Mnangagwa ya ce zai zama mai gaskiya ga Zimbabwe, tare da yin biyayya da karewa da martaba kundin tsarin mulkin kasar, da kuma biyayya ga sauran dokokin kasar.

Ranstuwar da aka yi a filin wasa na kasar, na zuwa ne bayan a ranar Juma'ar da ta gabata, kotun kundin tsarin mulkin kasar ta kori karar da shugaban 'yan adawa Nelson Chamisa ya gabatar mata, ya na mai kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata.

A cewar hukumar zaben kasar, Mnangagwa ya samu kaso 50.67 na kuri'un da aka kada, inda abokin adawarsa Nelson Chamisa ya samu kaso 44.3.

Chamisa ya kalubalanci sakamakon zaben ne bisa zargin ya kunshi kurakurai. Sai dai, kotun ta kori karar, ta na mai cewa shugaban 'yan adawar ya gaza gabatar da shaidun da za su tabbatar da ikirarinsa.

Nelson Chamisa dai ya kauracewa bikin rantsuwar da ya samu halartar dubban al'ummar Zimbabwe da shugabannin kasashen da Gwamnatocin Afrika da dama, ciki har da Shugaban Tarayyar Afrika kuma Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China