in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakiliya ta musamman ta shugaban kasar Sin ta gana da shugaban kasar Zimbabwe
2018-08-27 10:50:09 cri
Wakiliya ta musamman ta shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakiyar shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin Madam Su Hui,ta gana da shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa a birnin Harare a jiya Lahadi.

Madam Su ta isar da sakon gaisuwa da fatan alheri da shugaba Xi ya aikewa shugaba Mnangagwa, don taya shi murnar zama shugaban kasar Zimbabwe a sabon zagaye. Su ta ce, Zimbabwe ta samu nasarar gudanar da zaben shugaban kasa a kwanakin baya, al'amarin da ya shaida irin niyya gami da zabi da jama'ar kasar ke da su. Kasar Sin na maraba da halartar shugaba Mnangagwa taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC wanda za'a yi a watan Satumban bana a birnin Beijing, domin kara bunkasa huldar dake tsakanin Sin da Zimbabwe da Sin da Afirka baki daya.

A nasa bangaren kuma, Mnangagwa ya ce kasarsa da kasar Sin aminan juna ne na koda yaushe, kana kuma yana sa ran halartar taron kolin dandalin FOCAC da yin shawarwari da shugaba Xi Jinping, don tattaunawa kan inganta hadin-gwiwa tsakanin Afirka da Sin da Zimbabwe da Sin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China