Kawo yanzu, cutar da ta barke a makon da ya gabata a ungunwannin dake Glen View da Budiriro dake yawan al'umma, ya yi sanadin mutuwar mutane 20, yayin da 2,000 suka kamu da ita, kana ta kuma barke a wasu sassa na kasar.
Sabon Ministan lafiya na kasar Obadiah Moyo, ya shaidawa manema labarai cewa, gwamnati ta dauki matakan dakile yaduwar cutar, ciki har da hana tallar kifi da nama da kuma dakatar da karatu a wasu makarantun dake yankunan da cutar ta barke.
Ya ce an samu barkewar cutar ne sanadiyyar fashewar bututan kawar da najasa, abun da ya bata ruwan rijiyoyin burtsatsai da sauran rijiyoyin da mazaunan wurin ke amfani da su.
Yawancin mutanen da ke yankunan dake da yawan jama'a sun dogara ne kan ruwan rijiyoyi da na burtsatsai, saboda rashin samun tsafatatacen ruwa akai akai.
Ministan ya ce Gwamnati ta nemi taimakon hukumomin MDD da na kamfanoni masu zaman kansu, domin su samar da ruwa ga al'ummar yankunan da cutar ta barke.
Kafin wannan, lokaci na karshe da Zimbabwe ta fuskanci barkewar cutar kwalara shi ne shekarar 2008, inda ta yi sanadin mutuwar mutane 4,000 yayin da kusan 100,000 suka kamu da ita. (Fa'iza Mustapha)